Isa ga babban shafi
Jordan

Abu Qatada ya musanta tuhumar laifukan ta’addacin da ake yi mai

Fitaccen Malamim addinin Islaman da Britaniya ta mikawa kasar Jordan, Abu Qatada, ya musanta tuhumar da ake masa na laifufukan ta’adanci da aka chaje shi da shi.

Abu Qatada a lokacin da za a gurfanar da shi a gaba kotu
Abu Qatada a lokacin da za a gurfanar da shi a gaba kotu Reuters
Talla

Malamin wanda tun a shekarar 2002 Birtaniya ke kama shi, amma kotu ta wanke shi, ya yi watsi da tuhumar, inda lauyan sa Taysir Diab ya ce yau zai daukaka kara dan ganin an bada belinsa.

Birtaniya ta kwashe shekaru 10 tana neman korar sa daga kasar, amma kotu ta ki, har sanda suka shiga wata yarjejeniya da kasar Jordan.

Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin tsakanin kasashen biyu na nuna cewa ba za a tuhumi malamin ba a bisa bayanan da aka tatsa a wurinsa ta hanyar azabtarwa.

Qatada wanda ake danganta shi da Osama Bin Laden, ana tuhumar shi bisa ayyukan ta'addanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.