Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya ta ki amincewa da daukaka karar hana fitar da Qatada

Birtaniya ta ce bata amince da hukuncin daukaka kara ba na hana fitar da malamin addinin Islaman nan, Abu Qatada daga cikin kasar, inda take cewa za ta bi duk hanyar da ta kamata dan mayar da shi kasar sa.

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron REUTERS/Chris Radburn/POOL
Talla

Sakatariyar harkokin cikin gida, Theresa May ta sanar da haka a Majalisa, inda take cewa za su dauki iznin daukaka kara.

“Gwamnati taki amincewa da wannan hukuncin, kuma ina shaidawa majalisa cewar yanzu zamu nemi izinin dan daukaka kara a kotun koli, na biyu kuma ina shaidawa majalisa cewar na sanya hannu a wata yarjejeniyar hadin kai ta fanni shari’a da Jordan, wanda yake da matukar muhimmanci wajen taimakawa kasashen mu biyu, wadda kuma za ta taimaka mana wajen amfani da ita.” Inji May.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.