Isa ga babban shafi
Isra'ila-Syria

Isra'ila ta kai wa Syria hari da jiragen yaki

Rahotanni sun ce wasu jiragen yakin Isra’ila sun kai hare hare akan wani sansanin sojin kasar Syria domin dakile aika wa da makamai ga ‘Yan kungiyar Hezbollah ta Iran. Wannan kuma na faruwa ne a dai dai lokacin da tawagar kwararru da aka aika kasar ta Syria ke ikirarin kammala tattara makamai masu guba a wuri daya.

Jirgin yakin kasar Isra'ila
Jirgin yakin kasar Isra'ila AFP
Talla

Kafar yada labaran Telebijin ta Al–Arabiya ta ruwaito cewa Isra’ila ta kai harin ne a sansanin Sojin Syria da ke a lardin Latakia, kamar yadda kafar ta ruwaito cikin Jami’an kungiyoyin da ke sa ido ga rikicin Syria yana tabbatar da faruwar al’amarin.

Hare haren na Isra’ila na zuwa a dai dai lokacin da hukumar haramta amfani da makamai masu guba ke ikirarin ta tattara makaman Syria a waje daya.

Tawagar kwararrun sun kai ziyara ne a kasar Syria domin lalata makamanta masu guba, kuma a yau Juma’a ne wa’adin karshe da aka dibar wa kwararrun domin cim ma kudirin da ya kai su Syria.

Kasar Amurka ta ce ta na da kwarin gwiwar za a iya lalata makaman Syria ma su guba, nan da tsakiyar shekarar 2014 kamar yadda aka tsara.  Mataimakin Sakataren ma’aikatar tsaron kasar Thomas Countryman yace nan da karshen watan Yunin shekarar 2014 za a kammala aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.