Isa ga babban shafi
Syria-Kuwait

Ana gudanar da taron kungiyar Larabawa a kasar Kuwait

Yau talata ne aka buda taron kungiyar kasashen larabawa a kasar Kuwaiti, taron da ke mayar da hankali kan rikicin kasar Syria da kuma sauran batutuwa da suka shafi yankin.

Taron kungiyar kasashen Larabawa
Taron kungiyar kasashen Larabawa
Talla

A daidai lokacin da ‘yan kasar ta Syria ke neman kasashen Larabawan su samar masu da karin makamai, wasu majiyoyi na cewa kasar Saudiyya wadda ke daya daga cikin kasashen da ke marawa ‘yan adawar baya, tana fatar ganin an sake salo ne domin kawo karshen wannan rikici.

Manzon MDD a game da rikicin na Syria Lakhdar Brahimi, ya bayyana cewa har yanzu akwai yiyuwar za a iya warware wannan rikici ta hanyar siyasa, tare da yin kira da a kawo karshen yin amfani da makamai a rikicin.

Har ila yau rikicin da ake fama da shi tsakanin kasashen Saudiyya da Bahrain da kuma hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kasar Qatar a gefe daya, na daga cikin batutuwan da ake jin cewa taron na kasar Kuweiti zai mayar da hankali a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.