Syria-MDD
Babu ranar tattauna batun rikicin Syria-Brahimi
Manzon Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Kasashen Larabawa kan rikicin Syria Lakhdar Barahimi, yace a halin yanzu ba wata takamaimiyar ranar da za a ci gaba da tattauna tsakanin ‘yan adawa da kuma gwamnati, bayan rugujewar tattaunawar da aka kwashe tsawon lokaci ana yi a Geneva.
Wallafawa ranar:
Talla
Brahimi, wanda ke zantawa da manema labarai a kasar Kuwaiti inda ake shirin buda taron kungiyar Larabawa a gobe talata, an tambaye shi ko yana da niyyar sake kai ziyara a birnin Damascus a nan gaba, amma sai yace ba zai amsa wannan tambayar ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu