Isa ga babban shafi
Syria-Kuwait

‘Yan tawayen Syria sun nemi a basu makamai

‘Yan adawar kasar Syria sun yi kira ga kasashen duniya da su taimaka masu da makamai domin gaggauta kifar da gwamnatin Bashar Assad daga karagar mulki. Sai dai babba mai shiga tsakani a rikicin kasar Lakhdar Brahimi yana ganin salon sasantawa a siyasance shi ne mafita wajen kawo karshen rikicin Syria.

'Yan tawayen Syria dauke da makamai
'Yan tawayen Syria dauke da makamai REUTERS/Houssam Abo Dabak
Talla

Shugaban kawance kungiyoyi da kuma jam’iyyun adawa na kasar Syria Ahmad Jarba, wanda ke gabatar da jawabi a gaban taron Kungiyar Kasashen Larabawa a kasar Kuwaiti, yace bai kamata kasashen duniya su zura ido shugaba Bashar na ci gaba da kashe al’ummar kasar ba.
Duk da cewa akwai batutuwa da dama da zasu mamaye zaman taron na Larabawa, amma rikicin kasar Syria ne zai fi mamaye wannan taro na tsawon yini biyu, wanda ke zuwa a daidai lokacin da rikicin tsakanin Assad da kuma ‘yan adawa ya shiga shekara ta hudu.

Yerima mai jiran gado a kasar Saudiya kuma daya daga cikin kasashen da ke marawa ‘yan adawar Syria baya Salman Bin Abdul aziz, yace kasashen duniya sun yaudari masu adawa da Bashar Assad ta hanyar kin cika wasu alkawulla na taimako da suka dauka musamman ma kin samar masu da makamai.

Manzon Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar Larabawa kan rikicin na Syria Lakhadr Brahimi, ya fito fili karara inda ya bayyana adawarsa da ci gaba da bai wa ‘yan tawaye makamai, yana mai cewa ko yanzu akwai yiyuwar za a iya warware rikicin ta hanyar tattaunawa.

Sai dai wannan taro na bana, yana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sabani tsakanin kasashen Saudiya da Bahrain da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa tsakaninsu da Qatar inda har ma wadannan kasashe suka janye jakadunsu daga Qatar, kasar da suke zargi da yin shisshigi a cikin al’amurransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.