Isa ga babban shafi
Saudi-Arabia

Hamas ta gana da saudiya bayan shekaru biyu na takun saka

Shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinu, Khaled Meshaal ya gana da Sarkin Sudiya Salman a ziyarar da ya kai kasar domin gudanar da aikin Ummara. 

Shugaban Kungiyar Hamas Khaled Meshaal
Shugaban Kungiyar Hamas Khaled Meshaal Reuters
Talla

Ganawar da aka yi ta sama sama na zuwa bayan shekaru biyu da suka wuce na takun saka tsakanin bangarorin biyu kamar yadda kamfanin dillacin labaran SPA ya rawaito a yau asabar.

Tawagar ta Hamas da Meshaal ya jagoranta ta mika gaisuwar karamar salla ga masarautar kasar ta Saudiyya jim kadan da kammala sallar Eidi a jiya.

Tun a shekera ta 2013 ne dangatakar Saudiya da Hamas ta ja baya sakamakon goyon bayan da Saudiyan ta nuna na kifar da Gwamnatin Mohammed Morsi na Masar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.