Dagantakar Diflomasiya tsakanin Amurka da China
Kasar China a kokarin sake farfado da huldar Diflomasiya da Amurka ta aike da wani jami'in ta a Amurka,jami'in dake da nauyin share fage a wannan sabuwar tafiya tsakanin kasashen Amurka da China tun bayan nasarar Donald Trump a zaben shugabancin kasar.
Wallafawa ranar:
Ziyarar dake zuwa a wani lokaci da sabon Shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da fuskantar suka daga wasu kasashen Duniya aminan Amurka kan batuttuwa da suka hada da diflomasiya , siyasar Amurka zuwa kasashen Duniya.
Babban jami’in diplomasiya na kasar ta China a wannan ziyara a Amurka na a mataki na sharan fage domin shugabannin kasashen biyu su gana da juna nan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu