Shugaban Amurka zai yi ganawa da shugabanin yankin Asiya a ziyarar da ya soma
Shugaban Amurka Donald Trump, a wannan juma’a ya fara ziyara ta farko a yankin Asiya ziyarar da ake kallo da matukar muhimmanci saboda dalilai na tsaro da kuma tattalin arziki.A tsawon kwanaki 12, shugaba Trump zai ziyarci kasashen Japan, Koriya ta Kudu, China, Vietnam da kuma Philippines.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ziyara Shugaba Trump a yankin Asiya ita ce mafi tsaho da wani shugaban Amurka ya kai yankin Asia tun bayan ziyarar George bush a shekarun 1991 da 1992
Shugaban na Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai yi amfani da wanann dama domin halartar taron Gabashin Asia da za a gudanar a Phillipines. Sai dai ana bayyana cewa babban makasudin ziyara sa, ita ce batun cinikaya, tsraro da shirin Nukiliyar Korea ta Arewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu