Dakarun Turkiya sun daura tutar kasar a tsakkiyar birnin Afrin
Shugaban kasar turkiya Recep Tayyip Erdogan a yau lahadi ya bayyana cewa, mayakan Syriya dake samun goyon bayan gwamnatin Ankara sun yi nasarar kwace daukaci yankin tsakkiyar birnin 'Afrin, tingar mayakan kurdawa a yankin arewa maso yammacin kasar Syriya.
Wallafawa ranar:
Afrin dai ya kasance birnin dake fuskantar hare haren daga sojan Turkiya tun a ranar 20 ga watan Janairun da ya gabata, a kokain da kasar ke yi wajen ganin ta fatatakar dakarun sa kan kurdawa na kungiyar (YPG).
Rundunar sojan kasar ta Turkiya dai, a kan shafinta na Twitter ta watsa wani hoton videon dake nuna sojanta na rataya wata tutar kasar a wata barandar bene
Gwamnatin Ankara dai, na kallon kungiyar YPG ta kurdawa a matsayin kungiyar yan ta’adda, duk da cewa, dakarun kurdawan na samun nasu goyon baya ne, daga kasar Amruka, domin su yaki masu ikrarin jihadi na kungiyar ISIS a Syriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu