Isa ga babban shafi
Saudiyya-Iran

Saudiyya ta ce lokacin daukar mataki kan Iran ya yi

Sarki Salman bin Abdul Aziz na kasar Saudiyya ya bukaci kasashen Larabawa da su tashi tsaye domin kalubalantar abin da ya kira ‘’aikata laifufukan’’ da Iran ke yi bayan harin da aka kai wa wasu jiragen ruwa da ya haifar da cece-kuce a Yankin Tekun Fasha.

Yerima Mohamed Ben Salman (MBS) a birnin Riyad, ranar 19 ga watan nuwambar 2018.
Yerima Mohamed Ben Salman (MBS) a birnin Riyad, ranar 19 ga watan nuwambar 2018. Bandar Algaloud/Courtesy of Saudi Royal Court/Handout/Reuters
Talla

Sarkin yayin wannan kira ne wajen taron kasashen Yankin da kuma na kasashen da ke kungiyar hadin kan Musulmai a Birnin Makkah.

Sarki Salman ya ce rashin mayar da martini mai karfi daga Yankin ne ya bai wa kasar Iran damar cin karena ba tare da babbaka ba. Sarkin ya sake yin kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen kalubalantar mulkin ‘Yan Shi’a.

To sai a martanin da ta mayar a wannan juma’a, gwamnatin Iran ta zargi Saudiyya da raba kawunan kasashen muslumi da kuma na yankin domin taimaka wa babban mikiyin al’ummar yankin wato Isra’ila.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Seyed Abbas Mousavi, ya ce raba kawunan jama’a shi ne babban abin da gidan sarautar Saudiyya ke yi, kuma wannan rabuwar kawuna ba mai amfana da shi face Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.