Isa ga babban shafi
qatar - zabe

Qatar na zaben 'yan majalisar Shura karon farko

'Yan kasar Qatar sun fara kada kuri'a a zaben' yan majalisun Shura a karon farko a wannan Asabar, wanda ke matsayin wata alama ta dimokuradiyya ko da yake masu sharhi na ganin ba za ta kai ga sauya mulki daga dangin dake mulki ba.

Wasu mata dake kada kuri'u a zaben majalisar Shura karon farko a tarihin kasar 02/10/21.
Wasu mata dake kada kuri'u a zaben majalisar Shura karon farko a tarihin kasar 02/10/21. REUTERS - IBRAHEEM AL OMARI
Talla

‘Yan majalisun shuru 30 za’a zaba cikin wakilai 45, wanda a baya sarkin Qatar, Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani ke nadawa.

Masu lura da al'amura sun ce kudin tsarin mulkin kasar na shekarar 2004 ya tanada zaben amma aka jinkirtawa sai kuma a wannan karo da kasar ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.