Isa ga babban shafi
India

Mutane 12 sun mutu a turmutsutsun wajen ibadar mabiya Hindu a India

Akalla mutane 12 suka rasa rayukansu yayin wani turmutsutsu a wajen ibadar mabiya addinin Hindu da ke India da sanyin safiyar yau asabar.

Wani wajen ibadar mabiya Hindu a India.
Wani wajen ibadar mabiya Hindu a India. REUTERS/Sivaram V
Talla

Rahotanni sun ce turmutsutsun ya faru ne a wajen ibada na Vaishno Devi da ke yankin Kashmir yankin da mahukunta kasar suka kawata da manyan manyan wuraren ibadar Hindu duk da kasancewarsa mai rinjayen musulmi da fin kashi 90.

Wani ganau ya shaidawa AFP ta wayar tarho cewa da dama sun jikkata a turmutsutsun yayinda aka kwashe gawar mutum 12.

Rasa rayuwa a wuraren ibadi ko kuma wajen neman tubarraki ba sabon abu ba ne ga mafiya addinin na Hindu wanda ke da rinjayen yawan jama'a a kasar India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.