Manoman India sun kawo karshen boren da suka soma yau da shekara daya
Manoman kasar India da suka share kusan shekara daya suna bore tare da zaman dirshan domin nuna adawa da sabbin dokokin gwamnati kan fasalta tsarin noma da sayar da amfanin gonar da suka noma, sun kawo karshen zanga-zangar su a ranar Asabar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga kasar ta India na nuni cewa wasu daga cikin manoman sun kwashe shingayen da suka kafa, tare da tattara kayan da zummar komawa gidajen su bayan kusan shekara daya suna zaman dirshan.
A watan da ya gabata dai ne Firaministan kasar Narendra Modi ya sanya hannu a wasu dokoki dake baiwa kamfanoni masu zaman kan su a kasar ikon kula dama sa ido a sha’anin da ya shafi makomar albarkatun da manoma ke samarwar a ksauwannin ciki da wajen kasar.
Tuni dai gwamnatin kasar ta India ta bayyana shirin fara ba da tallafi ga iyalan manoman masu bore da suka rasa nasu yayin gagarumar zanga-zangar da ta gudana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu