Kotun India ta zartas da hukuncin kisa kan mutane 38 saboda harin 2008
Kotun India ta zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane 38 yau juma’a wadanda ke da hannu a harin bom din shekarar 2008 da ya kashe gomman jama’a a yammacin birnin Ahmedabad na kasar.
Wallafawa ranar:
Tun a ranar 8 ga watannan ne kotun ta birnin Gujarat cibiyar kasuwancin India ta samu mutane 49 da hannu a kaddamar da farmakin na 2008 wanda ya kashe mutane 56 amma kuma yayin zaman kotun na yau juma’a mai shari’a A R Patel, ya zartas da hukuncin kisa kan mutane 38 daga ciki.
Babban mai shiri'ar Amit Patel ya ce sauran mutum 11 cikin masu hannu a farmakin 49 an yanke musu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
Wata kungiya da ta kira kanta da mujahidin India ta dauki alhakin farmakin na shekarar 2008 wanda ta ce fansa ce kan rikicin 2002 a birinin na Ahmedabad da ya kashe musulmi kusan dubu guda.
Akalla mutane 80 aka fara tuhuma da hannu a farmakin na 2008 amma kuma Mr Patel ya ce tuni aka wanke wasu 28 yayinda sauran kusan kowannensu aka same shi da ko dai laifin kisan kai ko hannu a taimakon ayyukan ta’addanci.
Kusan shekaru 10 baya ne aka faro shari’ar wadda ta akalla mutane dubu 1 da 100 ke bayar da shaida gabanin kammala ta a yau juma’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu