Isa ga babban shafi

Kayakin agaji sun fara isa Afghanistan bayan girgizar kasa ta kashe mutane 1000

Kasashen duniya sun farar tura kayayyakin jinkai bayan girgizar kasar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu guda a kasar Afghanistan, dai dai lokacin da ministan wajen kasar Abdul Qahar Balkhi, ke cewa ba kadai kayakin agaji Kabul ke bukata ba, domin kuwa akwai bukatar kasashen duniya su shiga tattaunawa da mahukuntan kasar don cire takunkuman da aka kakaba ma ta. 

Agajin abinci da ya isa wani yanki na Afghanistan.
Agajin abinci da ya isa wani yanki na Afghanistan. AP - Ebrahim Noroozi
Talla

Ministan wajen na Afghanistan Abdul Qahar Balkhi ya bayyana cewa kasashen duniya musamman makota ciki har da Pakistan da Iran da kuma Qatar sun fara turo da kayan agaji, wanda tuni aka fara raba wa jama’a, yayinda wasu kasashen suka yi alkawarin bayar da nasu taimakon a nan ba da jimawa ba.

A makon jiya kakkarfar girgizar kasar ta dirarwa wasu yankuna na Afghanistan tare da halaka mutane fiye da dubu guda baya ga jikkata wasu tarin mutane.

Balkhi ya ce ko shakka babu hakan zai ragewa jama’a radadin da su ke fama da shi biyo bayan wannan iftila’i, wanda ya ke cewa halin da al'umma suka shiga manuniya ce kan yadda takunkuman da aka kakaba wa kasar ke haifar da mummunan tasiri ga rayuwar al’umma.

Ministan wajen na Afghanistan ya yi fatan kasashen duniya za su yi nazari domin shiga tattaunawa da mahukuntan kasar game da yadda za a taimakawa jama’a.

A cewar Abdul Qahar Balkhi yakamata duniya ta tuna cewa Afghanistan ta share tsawon shekaru 20 a cikin yaki, saboda haka akwai bukatar bai wa al’ummarta damar numfasawa.

Tun bayan kwace ikon da Taliban ta yi da mulkin Afghanistan cikin watan Agustan shekarar 2020, kasashen Duniya suka katse tallafin da su ke baiwa kasar tare da sake lafta mata takunkuman karya tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.