Isa ga babban shafi

Mabiya Shi'a miliyan 21 na gangamin ibadar Arba'een a Karbala

Akalla mabiya mazhabar Shi'a miliyan 21 daga sassan duniya ke ziyarar ibada a Karbala da ke kasar Iraqi, inda suka sanya bakaken kaya da kuma gangami domin tuna ranar da aka cika kwanaki 40 da kisan gillar da aka yiwa Imam Hussein, jikan Annabi Muhammad SAW, duk da rikicin siyasar da ya mamaye kasar Iraqi ayau.

Taron miliyoyin musulmi mabiya shi'a da ke gudanar da ibadar Arbaeen a Karbala da ke Iraqi, wato tunawa da cika kwanaki 40 da kisan Imam Hussein jikan fiyayyen halitta.
Taron miliyoyin musulmi mabiya shi'a da ke gudanar da ibadar Arbaeen a Karbala da ke Iraqi, wato tunawa da cika kwanaki 40 da kisan Imam Hussein jikan fiyayyen halitta. AFP
Talla

Shidai wannan gangami da aka saba yinsa kowacce shekara, yana nuna kawo karshen zaman makokin kwanaki 40 da kisan da sojojin Khalifa Yazid suka yiwa Imam Hussein.

Wannan biki na janyo maza da mata daga sassan duniya dake tafiya Karbala, inda aka binne Imam Hussein da dan uwansa Abbas, sanye da bakaken kaya domin nuna juyayinsu, kuma yana daga cikin taron ibada mafi girma a duniya.

Bayan annobar korona da ta kwashe shekaru biyu ta kuma hana tafiye tafiye, akalla mutane miliyan 21 da dubu 200 aka bayyyana cewar sun halarci birnin a wannan mako, kamar yadda hukumomin dake kula da bakin suka sanar, kuma daga cikin su akwai baki yan kasashen waje miliyan 5 dake dauke da yan kasar Iran miliyan 3, adadi mafi yawa da aka taba gani.

Masu ziyarar ibadar na amfani da tazarar dake tsakanin kabarin Imam Hussein da na Abbas wajen yin addu’oi, yayin da maza kan dinga dukar kirazansu, wasu kuma suna zagaye kaburburan dauke da bakaken tutocin dake dauke da hotunan Imam Hussein.

Tun bayan kifar da gwamnatin Saddam Hussein a shekarar 2003 sakamakon yakin da Amurk ata jagoranta, an samu karuwar mabiya Shiar dake halartar bikin da ake kira Arbaeen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.