Isa ga babban shafi

'Yan Shi'a sun yi taron alhinin rasuwar Imam Hussain a Karbala

Dubban mabiya Shi'a  sun gudanar da taron Ashura a birnin Karbala na kasar Iraqi domin nuna alhinin game da zagayowar ranar kisan da aka yi wa Imam Hussain, jikan Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.

Wasu mabiya Shi'a da ke nuna alhinin kisan da aka yi wa Imam Hussain.
Wasu mabiya Shi'a da ke nuna alhinin kisan da aka yi wa Imam Hussain. AFP - HUSSEIN FALEH
Talla

Domin nuna alhinin rasuwarsa a shekara ta 680, mabiya Shi'a sanye da bakaken tufafi sun yi ta dukan kirjinsu, yayin da wasu kuma suka yi ta yan-yanke jikinsu da takubba da wukake.

Miliyoyin mutane daga kasashen Afghanistan da Pakistan zuwa Iran da Lebanon ke gudanar da bukukuwan kowace ranar 10 ga watan Muharam na addinin Islama wato ranar Ashura.

Mazahaba Shi’a dai na wakiltar sama da kashi 10 ne cikin 100 na al’ummar Musulmin duniya biliyan 1 da miliyan 800.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.