Isa ga babban shafi

China: Covid-19 ta kashe mutane dubu 13 a cikin mako guda

China ta sanar da cewa kusan mutane dubu 13 ne suka mutu sakamakon harbuwa da cutar Covid 19, bayan da wani babban jami’in lafiya a kasar ya ce aksarin ‘yan kasar sun kamu da cutar mai sarkafe numfashi.

Marasa lafiya a daya daga asibitocin kasar  China.
Marasa lafiya a daya daga asibitocin kasar China. AP - Andy Wong
Talla

Wannan adadi na wadanda suka mutu sakamakon harbuwa da cutar Covid 19   na zuwa ne mako guda bayan da China din ta ce kusan mutane dubu 60 ne suka mutu a cikin sama da wata guda bayan cutar ta kama su.

A wata sanarwa da ta fitar,  cibiyar yaki da cutuka ta kasar China ta ce a Asabar, marasa lafiya 681 da aka kwantar a asibiti  sun mutu sakamakon matsalar numfashi da cutar Corona ta haddasa, kana ddubu 11 da 977 sun mutu bayan sun kamu da saurian cutuka.

Wannan adadi dai bai hada da wadanda suka mutu a gida ba.

Wani kamfani mai zaman kansa da ke hasashe a kan wannan annoba, ya yi kiyasin cewa adadin wadanda wannan cuta za ta rika lakumewa a duk rana zai kai dubu 36 a wannan lokaci na hutun sabuwar shekarar Sinawa.

Kamfanin ya kuma yi kiyasin cewa sama da mutane dubu dari 6 ne suka mutu sakamakon harbuwa da wannan cuta tun da China ta yi watsi da shirin  tsaurara matakan kariya daga cutar a watan Disamba

Miliyoyin mutane ne suka yi balaguro a fadin kasar Sin a cikin kwanakin nan  don hadewa da ‘yan uwa da abokan arziki a wannan biki na sabuwar shekarar Sinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.