Isa ga babban shafi

China ta kawo karshen killace baki matafiya saboda Korona

Kasar China ta kawo karshen kebance matafiya da ta ke yi na tsawon kwanaki kafin shiga cikinta, matakin da mahukuntan kasar suka shafe kusan shekaru uku suna aiwatarwa domin dakile yaduwar annobar Korona.

Wasu baki da ke kan hanyar zuwa cibiyar killace masu fama da cutar corona a kasar China.
Wasu baki da ke kan hanyar zuwa cibiyar killace masu fama da cutar corona a kasar China. REUTERS - KIM HONG-JI
Talla

A Hong Kong, inda aka sake bude kan iyakar yankin da kasar ta Sin bayan shafe shekaru a rufe, mutane fiye da dubu 400 ne ake sa ran za su shirya yin balaguro zuwa arewa wato cikin kasar ta China, cikin makwanni takwas masu zuwa.

Tun cikin watan Disambar da ya gabata, gwamnatin China ta fara janye dokokin takaita walwalar jama’a don hana yaduwar cutar Korona, dokokin da a baya suka wajabta kulle ga miliyoyin mutane, baya ga kebe baki matafiya da wadanda suka yi mu’amala da su tsawon makwanni.

Dokokin takaita walwalar dai sun yi tasiri ainun kan tattalin arzikin kasar ta China, wanda shi ne na biyu mafi girma a duniya, lamarin da ya tunzura dubun dubatar Sinawan da suka gudanar da zanga-zanga fadin kasar, kafin daga bisani a samu sassauci.

Tuni dai ‘yan China da dama suka shiga shirin yin balaguro zuwa kasashen waje, bayan matakin gwamnati na kawo karshen kebanci baki da sauran matafiya da ke komawa kasar tsawon makwanni.

Sai dai karuwar yawan masu kamuwa da cutar Korona cikin makwannin baya bayan nan a China, ya sanya kasashe fiye da 12 akasarinsu na Turai, daukar matakin aiwatar da gwajin Korona na tilas a kan matafiya daga kasar ta Sin, gudun kada a koma gidan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.