Isa ga babban shafi

Karin kasashe sun sanya takunkumi kan baki 'yan China saboda Korona

Kasashe da yankuna fiye da 12 sun dauki  matakin maido da dokokin tsaurara bincike kan baki daga China, sakamakon yadda rahotanni ke fitowa daga kasar kan yadda ake samun karuwar adadin mutanen da ke kamuwa da cutar Korona.

Matafiya a filin jiragen sama na Beijing babban birnin kasar yayin da cutar Korona ke sake yaduwa a sassan kasar. 27 ga Disamba, 2022.
Matafiya a filin jiragen sama na Beijing babban birnin kasar yayin da cutar Korona ke sake yaduwa a sassan kasar. 27 ga Disamba, 2022. © REUTERS/Tingshu Wang
Talla

Australia da Canada ne kasashe na baya bayan nan, da suka bayyana cewar daga yanzu ya zama tilas dukkanin wasu baki daga China, Hong Kong da kuma Macao su gabatar da sahihin sakamakon gwajin da ke nuna cewar ba sa dauke da cutar Korona.

Kwararrun masana lafiya na kasa da kasa sun yi gargadin cewa, mai yiwuwa miliyoyin mutane ne ke kamuwa da cutar Korona kowace rana a kasar ta China, tun bayan da gwamnatin kasar ta janye dokokin takaita walwalar da aka shafe tsawon lokaci ana aiki da su a kasar domin dakile yaduwar annobar ta Korona.

Ministan lafiyar Australia Mark Butler, ya bayyana rashin gamsassun bayanan da gwamnatin China ke fitarwa kan sake yaduwar cutar Korona a matsayin dalilin da ya sa suka dauki matakin tsaurara matakan ba da izinin shiga kasarsa da baki daga kasar ta Sin.

Sauran kasashen da suka dauki matakin tilasta gabatar da shaidar rashin cutar Korona, ko kuma gwaji nan take ga baki ‘yan China kafin shiga cikinsu, sun hada da Birtaniya, Faransa, italiya, Spain India, Japan, Korea ta Kudu, da kuma Taiwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.