Isa ga babban shafi

Covid-19: Hukumomin lafiya sun nuna fargaba kan matakin da China ta dauka

Masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa akwai yuwuwar a kara samun sabbin nau’ikan cutar Covid-19 daga China, yayin da kasar ta dauki matakan kawo karshen wannan cuta da kuma gwajin gano masu dauke da ita.

Wani mai fama da cutar Corona kenan lokacin da yake karbar kulawa a asibiti
Wani mai fama da cutar Corona kenan lokacin da yake karbar kulawa a asibiti © DR
Talla

A wannan makon ne kasar China ta sanar da cewa za a daina killace masu balaguro zuwa kasar daga ranar takwas ga watan janairu, karon farko kenan da ta dauki wannan matakin tun bayan bullar cutar.

Dai dai lokacin da ma’aikatar lafiya ta kasar ta dakatar da fitar da sakamakon gwajin kwayar ciutar, hukumomi daga biranen kasar sun yi kiyasin cewa dubban mutane ne suka harbu da cutar a ‘yan makwannin nan, inda asibitoci ke cike da masu fama da Covid-19 din

Yayin da kwayar cutar a yanzu tana iya yaduwa tsakanin kusan kashi daya cikin biyar na al'ummar duniya da kusan dukkansu ba su da rigakafi, masana na fargabar China za ta zama kasar da za ta rika samar da sabbin nau’ikan kwayar wannan cuta.

Antoine Flahault, darektan Cibiyar Kiwon Lafiya ta Duniya a Jami'ar Geneva, ya shaida wa AFP cewa kowace sabuwar cuta na iya haifar da nau’ikan kwayar cutar.

Wannan mataki na China ya sa kasashen Amurka, Italiya, Japan, Indiya da kuma Malaysia fitar da sanarwar cewa za su kara matakan gwajin kwayar cutar, musamman ga matafiyan da suka fito daga kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.