Isa ga babban shafi

Har yanzu jiragen yakin China basu bar iyakarmu ba - Taiwan

Ma’aikatar tsaron Taiwan ta ce har yanzu akwai ragowar jiragen yakin China na ruwa da na sama da ke shawagi a kusa da Tsibirin, kwana guda bayan da kasar ta Sin ta sanar da kawo karshen atasayen sojin da ta shafe kwanaki uku tana yi, domin mayar da martani kan alakar yankin da Amurka.

Wasu jiragen yakin China a kusa da yankin Taiwan.
Wasu jiragen yakin China a kusa da yankin Taiwan. AP
Talla

A ranar Litinin kasar Sin ta kawo karshen atasayen soji na kwanaki uku a kusa da Taiwan, inda ta bayyana gamsuwa da gwajin karfin sojan da ta yi, a karkashin shirin kaddamar da yaki da kuma yi wa yankin da ta ke kallo a matsayin na ta kawanya.

Sai dai gwamnatin tsibirin na Taiwan ta mayar da martani da cewar ba za ta sassautawa kan shirinta tunkarar yaki da kasar ta Sin ba, wadda take sa ido akan duk wani motsi na dakarunta.

A ranar Asabar da ta gabata China ta fara atisayen sojin ruwa da na sama a kusa da Taiwan, bayan da shugabar yankin Tsai Ing-wen ta koma gida daga Amurka, inda ta gana da kakakin majalisar wakilan kasar Kevin McCarthy a Los Angeles.

China dai na cigaba da ikirarin cewa yankin na Taiwan a karkashinta yake, abinda ya sanya a ranar Litinin ta yi gargadin cewa ba zai yiwu tsibirin ya samu zaman lafiya da kuma ‘yancin zama kasa ba a lokaci guda, don haka zabi ya rage wa mahukuntan yankin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.