Isa ga babban shafi

Taliban sun hana mata ziyartar gidajen gyaran jiki da gashi a kasar

Gwamnatin Taliban da ke a Afghanistan, ta bayar da umarnin rufe gidajen ado da gyaran jiki na mata cikin wata a duk fadin kasar. Wannan dai na daga jerin matakan da Taliban ke dauka domin tabbatar da cewa mata sun kasance a cikin gida da kuma kaurace wa wuraren taruwar jama’a. 

یک سالن زیبایی در کابل. افغانستان /  25 آوریل 2021
یک سالن زیبایی در کابل. افغانستان / 25 آوریل 2021 AP - Rahmat Gul
Talla

Aiwatar da matakin a cikin wata daya, na nufin cewa ko baya ga hana mata fita zuwa wurare na musamman da aka kebe domin ado da gyaran jiki, dubban mata za su rasa ayyukan yi a Afghanistan. 

Wata mata da ta mallakin shagon ado da gyaran jiki, ta bayyana nadama a game da kasancewarta ‘yan asalin kasar Afghanistan, inda ta ci gaba da cewa, ta yin adama da Allah ya kaddari aka haife ta a kasar. 

A lokacin da ta karbi ragamar mulki a shekara ta 2021, Taliban da farko ta dauki matakin hana mata yin karatu har zuwa matakin jami’a, tare da hana su shiga filayen da aka kebewa jama’a domin shakatawa da kuma wuraren motsa jiki. 

Tuni dai gwamnatin Taliban ta hana mata yin aiki a karkashin kungiyoyi masu zaman kansu, ciki har da na Majalisar Dinkin Duniya, yayin da aka sallami dubban mata daga aikin gwamnati inda aka ba su hakkokinsu tare da umartar su da su zauna a gida. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.