Isa ga babban shafi

Matan Afghanistan na zanga-zanga kan dokar haramta shagunan gyaran jiki

Jami’an tsaron Afghanistan sun yi amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa dandazon matan da ke zanga-zangar kalubalantar matakin gwamnatin Taliban na kulle ilahirin shagunan gyaran jikin da ke sassan kasar.

Wasu shagunan gyaran jiki a birnin Kabul.
Wasu shagunan gyaran jiki a birnin Kabul. AP - Rahmat Gul
Talla

Wannan yunkuri na Taliban da ke matsayin na karshe wajen kange matan daga duk wata rayuwa a waje bayan hana musu aiki da karatu, ya gamu da fishin dubunnan matan kasar ta Afghanistan lura da yadda kulle shagunan gyaran jikin zai dankwafe rayuwar miliyoyin iyalai da suka dogara da kananun sana’o’I wajen tafiyar da harkokinsu.

Tun bayan da Taliban ta kwace iko a Afghanistan cikin watan Agustan 2021, rayuwar mata ta fada garari ta yadda karkashin dokokin da suka gindaya matan ke fuskancin haramcin ganinsu a duk wasu wuraren shakatawa ko na nishadi ko wuraren motsa jiki baya ga uwa uba manyan makarantu da jami’o’i da kuma wuraren aiki, baya ga tilasta musu rufe ilahirin jikinsu idan bukatar fita ta taso.

Hukuncin baya-bayan nan da ya shafi rayuwar matan na Afghanistan shi ne na watan jiya da Taliban ta bukaci kulle ilahirin shagunan gyaran jikin da ke kasar, wanda ke matsayin dama daya tal da ta ragewa matan samun sukunin iya ganin kansu a waje don gani gari.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa akalla matan da yawansu bai gaza 50 ba ne suka fita kan titin Butcher na birnin Kabul don kalubalantar wannan haramci na Taliban a wani yanayi da ba safai aka saba gani a kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.