Isa ga babban shafi

Japan ta yi bikin cika shekaru 78 da harin nukiliya da Amurka ta kai mata

Japan ta gudanar bikin tunawa da ranar da Amurka ta jefa mata makamin Nukiliya a yankunan Hiroshima da Nagasaki, abin da ya kawo karshen yakin duniya na biyu. 

Firaministan Japan  Fumio Kishida a yayain addu'o'in tunawa da  ranar daa aaka kai wa Hiroshima da Nagasaki hari, 6 Agusta, 2023.
Firaministan Japan Fumio Kishida a yayain addu'o'in tunawa da ranar daa aaka kai wa Hiroshima da Nagasaki hari, 6 Agusta, 2023. AP
Talla

 

Ranar 6 ga watan Agustan 1945 ne Amurka ta yake shawarar kai wannan hari da shiga cikin tarihin muggan hare-hare na duniya wanda har yanzu al’ummar Japan na fama da tasirin sa. 

Bikin na bana wanda shine karo na 78 ya mayar da hankali ne kan yadda za’a takaita irin barazanar da kasashen duniya ke yi na mallakar makamin nukiliya koma amfani da shi. 

Da yake karanta wata makala a wajen bikin taron tunawa da wannan rana mahajin garin Hiroshima Kazumi Matsui ya bukaci duniya ta kara matsa lamba, wajen haramta amfani da wannan shu’umin makami. 

Kamar yadda aka saba, an kada kararrawar zaman lafiya da misalin karfe 8:15 na Safiya wadda ke alamta cewa ranar da al’ummar kasar suka gamu da mummunan tashin hankali ta zagayo. 

Tarihi ya nuna cewa da misalin karfe 8:15 safiyar ranar 6 ga watan Agustan 1945 ne kwararren mai iya sarrafa makamin Nukiliyan Enola Gay ya harba makamin da kai tsaye ya dira a garin Hiroshima kafin ranar 9 watan Agustan wannan shekara dai kara jefa wani zuwa garin Nagasaki, harin da ya lakume rayukan mutane dubu 129 zuwa dubu dari 226. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.