Isa ga babban shafi

India: A kalla mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon ruwan sama

A  kalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu a Indiya, wadanda suka hada da guda 9 da suka rasa rayukansu,  karkashin rugujewar da wani ginin da ake gudanar da bautar addini a cikinsa ya yi, a yayin da wasu gomman mutane kuma suka bata, bayan  sakar ruwan sama mai yawa,  da ya haifar da ambaliya  tare da zaftarewar kasa, a cewar mahukumta.

Dans l'Etat du Bihar le bilan est lourd : plus de deux millions de personnes sont déplacées et des centaines de villages sous les eaux.
Dans l'Etat du Bihar le bilan est lourd : plus de deux millions de personnes sont déplacées et des centaines de villages sous les eaux. (Photo : AFP)
Talla

Mamakon ruwan da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi, ya ruguza gadoji da kuma gidajen zaman jama’a, tare da yin awan gaba da motoci a jihar  Uttarakhand da  Himachal Pradesh, dake arewacin kasar.

Duk dai a wannan lokaci na markar damina, ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa sun kasance a kullum masu haifar da katafariyar barn aga dukiya da rayukan jama’a. a cewar masana, ruwan na marka na ci gaba da yawa a ko wane lokaci sakamakon sauyin yanayin da duniya ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.