Fadan Siyasar Da Ya Barke A Kyrgyzstan
Litinin din nan babu abin da ake gani a titunan birnin Osh na kasar Kyrgyzstan dake makwabtaka da Uzbek sai gawarwakin mutane da aka kone kurmus,yayin da mazauna yankin ke boyewa, cikin halin tsananin firgici da ake faman kone gine-gine da harbe-harbe.Kwanaki uku kena aka kwashe cur ana kafsa fada tsakanin al’umomi, wanda ya yi sanadiyyar mutane da dama, tare da yin sanadiyyar kauracewar dubunnan ‘yan kabilar UzbekA yayin da kasashen duniya ke nuna matukar damuwa da wannan tashin hankali da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane dari da goma sha bakwai, wasu kimanin dubu suka jikkata, ‘yan kabilar Uzbek dake cewar yawan wadanda aka kashe yafi haka, sun zargi dakarun gwamnati da cewa suna taimaka wa ‘yan ta’addan Kyrgyzstan.
Wallafawa ranar: