Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiyya ta haramta wa jirgin sojin Isra’ila wucewa ta sararin samaniyarta

Kasar Turkiyya ta haramta wa wani jirgin sojin Isra’ila wucewa ta sararin samaniyarta, matakin da ake yi wa kallon wata ramuwar gayya ce ta harin da Isra’ila ta kai kan tawagar masu kai kayan agaji zuwa Gaza a watan jiya.Sai dai an kafa kwamitin binciken wannan hari, kuma shi kansa Firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu shi ne zai fara ba da shaida.Wani jami’in jakadancin Turkiyya ya fada yau litinin cewa wannan jirgi an haramta masa wucewa, kuma za a dauki mataki kan duk wani jirgin sojin Isra’ilan da zai yi shawagi a sararin samaniyar Turkiyyan.Ya ce wajibi ne kowane jirgin soji ya karbi izinin wucewa, yayin da Firayi ministan Turkiyya ya tabbatar da cewa an kafa dokar haramcin shawagin ne sakamakon harin ranar 31 ga watan Mayu.  

Firayi Ministan Turkiyya
Firayi Ministan Turkiyya رویترز
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.