Isa ga babban shafi
Iran-Switzerland

Iran ta gaiyaci Jakadan Switzerland

HUKUMOMIN Kasar Iran, sun gaiyaci Jakadan Kasar Switzerland, Georg Steiner, dan bayyana korafinsu kan zargin sace wani masanin fasahar nukiliya da Amurka ta sace, wato Shahram Amiri.Wannan ya biyo bayan wasu hotunan vidi’o da ya nuna masanin na bayani cewar, Hukumomin Amurka suka sace shi, kuma yana hannunsu.Kasar Switzerland ke gudanarwa amurka aiyukan diplomasiya a Iran, saboda rashin hulda kai tsaye tsakanin kasashen na shekaru 30.Iarn tace, tana da yakinin cewar, masanin Shahram Amiri na tsare a Amurka.  

Shahram Amiri
Shahram Amiri AFP/PRESS TV
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.