Isa ga babban shafi
Japan

Nagasaki a kasar Japon cikon shekaru 65 da jefa bomb ta biyu da kasar Amurika ta yi

Bayan shekaru 65 da kasar Amurika ta jefa bomb ta biyu a garin Nagasaki a lokacin yakin duniya na biyu ,kwanaki kalilan bayan jefa ta farko a garin Hiroshima a ranar 6 ga watan Ugusta,a yau garin Nagasaki ya kasance garin bukukuwan juyayi na lamarin da ya gudana.Wakillan kasashe guda 32 ne daga bangarorin duniya daban-daban su ka samu hallarta.A karon farko kasar Franshu da ta Britaniya sun aika manzanni na musananm a wurin bukukuwan.Kasar Amurika da ta tura jakadanta John Roos a garin Hiroshima bai hallarci bukukuwan juyayin garin Nagasaki ba.Ganin cewa jefa wanan bomb ya kawo karshen yakin duniya na biyu tare da hallaka mutane sama da dubu dari 2 da 10, yawancin su fararen hulla,kasar Amurika ba ta taba nuna wata ladamaba kan maganar neman gafara dangance da wanan lamari da ya gudana a shekara ta 1945. 

Jirgin yakin ruwan kasar Japan
Jirgin yakin ruwan kasar Japan AFP /JAPAN POOL
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.