Eritrea-MDD
MDD ta kakubawa Eritrea takunkumi
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kakubawa kasar Eritrea sabbin takunkumi, saboda zargin da ake mata na taimakawa kungiyar Al Shabab, tare da goyon bayan harin ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Talla
Kasashe 13 daga cikin 15 da ke Majalisar suka amince da takunkumin, sai dai kasashen Rusha da China suka kauracewa Majalisar.
Bukatar Najeriya da Gabon na ganin an hana masu zuba jari a ma’adinan kasar da kuma hana ‘Yan kasar da ke zama a kasashen duniya aikawa da kudi gida, bai samu goyan baya ba a Majalisar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu