Isa ga babban shafi
Turkiya-Faransa

Jekadan Turkiya ya koma Faransa bayan samun sabani tsakanin kasashen

Jakadan Kasar Turkiya a Faransa, Tahsin Burcuoglu, ya koma birnin Paris, bayan janye shi da gwamnatin kasar ta yi, sakamakon kuri’ar da Majalisar wakilan Faransa suka kada, na amincewa da kisan kiyashin da Turkiya ta yi wa Armeniyawa.

Fira Ministan Turkiya  Tayyip Erdogan  lokacin da ya ke jawabin nuna adawa da kada kuri'ar gasgata musanta kisan Armeniyawa
Fira Ministan Turkiya Tayyip Erdogan lokacin da ya ke jawabin nuna adawa da kada kuri'ar gasgata musanta kisan Armeniyawa Reuters/Umit Bektas
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Selcuk Unal, yace Jakadan ya kammala tattauna da Gwamnatin kasar, kuma yanzu haka, ya koma bakin aikinsa.

Gwamnatin Turkiya ta janye jekadanta ne, Burcuoglu bayan da karamar Majalisar Faransa ta amince da dokar da ke adawa da musanta kisan kiyashin da Turkiya ta yi wa Armeniyawa. Amma kuma yanzu jekadan ya koma ga aikinsa domin kokarin ganin majalisar dattijai bata amince da kudirin dokar ba.

‘Yan adawa a kasar Faransa sun soki lamarin inda suka danganta al’amarin da takun Siyasar shugaba Sarkozy domin samun amincewar Armeniyawa mazauna kasar Faransa a zaben shugaban kasa da za'a gudanar.

A ranar 22 ga watan Disemba ne karamar majalisar ta kada kuri’ar amincewa da dokar yanke hukuncin dauri da cin tarar duk wani mutum da ya nemi musanta kisan kiyashin a shekarar 1915 a zamanin mulkin shugaba Othman.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.