Isa ga babban shafi
G20-Girka

Kasashen G20 za su gana bayan samun nasarar zaben Girka

Shugabannin kasashe 20 masu karfin Tattalin arzikin duniya zasu gana a kasar Mexico domin tattauna hanyoyin magance matsalar tattalin arziki da ke addabar wasu kasashen Turai. Kasashen za su gana tare da karfin gwiwar nasarar da Jam’iyyar da ke goyon bayan kudirin IMF da kasahsen Turai ta samu a zaben ‘Yan Majalisun Girka.

Hotunan Fuskokin wasu shugabannin kasashen G20 da suka daha da Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma da Shugaban Faransa Francois Hollande, da Fira ministan Indiya Manmohan Singh,  sai kuma shugaban Amurka  Barack Obama wadanda zasu halarci taro a kasar Mexic
Hotunan Fuskokin wasu shugabannin kasashen G20 da suka daha da Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma da Shugaban Faransa Francois Hollande, da Fira ministan Indiya Manmohan Singh, sai kuma shugaban Amurka Barack Obama wadanda zasu halarci taro a kasar Mexic
Talla

Sakamakon zaben Girka ya nuna kasar za ta ci gaba da zama a kungiyar kasashen Turai.

Tuni dai kasuwar hannayen jarin kasashen Turai da Yankin Asiya suka tashi saboda sakamakon zaben kasar Girka.

Rahotanni sun ce Fira ministan kasar Spain Mariano Rajoy ya zanta da takwarorin shi na Britaniya da Faransa da Jamus da Italia ta wayar Salula game da nasarar da aka samu a kasar Girka tare da jaddada ci gaban a matsayin wani matakin ceto kudin euro.

Ana saran kasashen BRICS, d suka hada da Brazil, Rusha da Indiya da China da Afrika ta kudu, za su amince da kudirin ba Hukumar bada lamuni ta duniya, Dala Biliyan 60 a taron, daga cikin Biliyan 430 da hukumar ke bukata daga kasashen G-20.

Shugaban Bankin Duniya, Robert Zoellick, yace matsalar bashin kasashen Turai ya haifar da ci bayan kasuwannin hannayen jari a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.