Isa ga babban shafi
Venezuela

‘Yan adawa suna koke a Venezuela saboda alamun jinkirin rantsar da Chavez

Gwamnatin kasar Venezuela tace za ta dage bukin rantsar da Hugo Chevez har sai Shugaban ya samu karfin jikin shi daga jinyar tiyatar da aka yi ma shi. ‘Yan adawa a kasar Sun bukaci kotun koli ya yanke hukunci akan bukin rantsuwar domin ya sabawa kundin tsarin mulki.

Wani dan kasar Venezuela dauke da hoton Hugo Chavez
Wani dan kasar Venezuela dauke da hoton Hugo Chavez REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

A sanarwar da Gwamnatin kasar ta bayar an bayyana Chavez ba zai iya fitowa bukin rantsar da shi ba a ranar Alhamis har sai ya murmuje nan da ‘yan kwanaki ya karbi rantsuwar a gaban kotun Koli.

Shugabannin Jam’iyyar Chavez sun ce ana iya jinkirta rantsar da shugaban har sai ya samu sauki kamar yadda wani sashen Kundin tsarin mulkin kasar ya bayar da dama.

Rahotanni sun ce rashin lafiyar Chavez ta yi tsanani domin yana fama da matsalar huhu da daukewar numfashi bayan an yi masa tiyatar Cancer.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.