Isa ga babban shafi
Venezuela

Dubban Masoya Chavez sun rantsar da shi yana gadon Asibiti

‘Yan kasar Venezuela, sun dauki rantsuwar amincewa da Shugabancin Hugo Chavez da ke jinyar cutar Cancer ko sankara a wani Asibitin kasar Cuba. Mataimakin Shugaban kasar Nicolas Maduro ne ya jagoranci taron mutanen, tare da karanta rantsuwar, Dubun dubatar jama’a kuma suna amsawa.

Dubban masoya Shugaban Venezuela Hugo Chavez à wani gangamin ratsar da shi da suka hada a Caracas
Dubban masoya Shugaban Venezuela Hugo Chavez à wani gangamin ratsar da shi da suka hada a Caracas REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Dubban masoya Chavez sun ta yekuwar fatar samun lafiyar shi tare da ci gaba da ba shi goyon baya.

Mataimakin Shugaban kasar ya yi kira ga ‘Yan sanda su sa ido matuka ga ‘yan adawa, da ya zarga da kokarin juyin mulki.

A Taron mutanen sun rera taken kasar Venezuela tare da jinjina ga shugabannin Bolivia Evo Morales da shugaban kasar Uraguay Jose Mujica da kuma hambararren shugaban kasar Paraguay Fernando Lugo.

‘Yan adawar kasar dai sun yi kiran gudanar da wani gangami a ranar 23 ga watan Janairu, ranar da ake gudanar da bukin Demokradiyya a kasar, domin adawa da jinkirin rantsar da Chavez.

A ranar 10 ga watan Janairu ne ya dace a rantsar da Chavez amma kotun kolin kasar ta bayar da umurnin dage rantsuwar har sai shugaban ya samu lafiya, matakin da ‘yan adawa suka ce ya saba wa dokar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.