Isa ga babban shafi
Venezuela

Lafiyar Chavez na cikin mawiyacin hali, inji tsohon mataimakin shugaban kasar

Tsohon mataimakin shugaban kasar Venezuela, Elias Jaua, ya ce, lafiyar shugaban Hugo Chavez na cikin wani mawiyacin hali, bayan aiki da aka mai na cutar Cancer a can kasar Cuba, inda ya je neman magani. Sai dai duk da haka, rashin kasancewar a kan kujerar mulkin kasar na jawo takaddama yayin da ‘Yan adawa a kasar ke ta da jijiyar wuya.  

Wani masoyin shugaba Hugo Chavez rike da hotonsa
Wani masoyin shugaba Hugo Chavez rike da hotonsa REUTERS/Jorge Silva/Files
Talla

“Yanayin na da rudani, lallai ne shugaba Hugo Chavez na fama da murmurewa daga wannan aiki da aka mai.” Inji Jaua, wanda ya rike mukamain mataimakin shugaban kasara a watan Janairun shekarar 2010 zuwa Oktoban shekarar.

A dai ranar asabar din da gabata ne, Mataimakin Chavez, har ila yau wanda ake ganin zai maye gurbinsa idan har wani abu ya faru, ya ziyarci shi.

Haka zalika, wani dan uwan Chavez ya musanta, rade-raden da ake na cewa, Chavez ya fada cikin wata doguwar suma.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.