Isa ga babban shafi
Algeria-Mali

Kasashen Duniya sun shiga damuwa bayan mutuwar Mutanen da aka yi garkuwa da su a Algeria

Gwamnatocin kasashen Turai da wasu kasashen Duniya sun bayyana damuwarsu game da makomar ‘Yan kasashensu da ‘Yan Bindiga suka yi garkuawa da su a Algeria bayan mutuwar wasu da dama a yunkurin kubutar da su.

Wani Allo da ke dauke da bayani game yankin Sahara na Amenas a Algeria
Wani Allo da ke dauke da bayani game yankin Sahara na Amenas a Algeria Reuters/Kjetil Alsvik/Statoil/Handout
Talla

Ministan yada Labaran kasar Algeria yace mutane da dama ne suka mutu amma an samu nasarar kubutar da wasu daga cikinsu wadanda yawancinsu suka samu rauni.

Daruruwan Mutane ne ‘Yan bindiga da aka ruwaito suna da Alaka da kungiyar Al Qaeda suka yi garkuwa da su a wani Kamfanin Mai da ke yankin Amenas tare da kiran kawo karshen yaki a Mali kafin su mika mutanen da ke hannunsu.

Mahukuntan Algeria sun ce kimanin ma’aikatan kasar 600 ne aka kubutar daga hannun ‘Yan Bindiga tare da Turawa guda Hudu daga kasashen Birtaniya da Faransa da kuma wasu ‘Yan kasar Kenya.

Rahotanni sun ce kimanin ‘Yan kasashen Waje 41 ne ke hannun ‘Yan bindiga 'Yan kasashen Birtaniya da Faransa da Italiya da Japan da Norway da kuma Amurka.

Tuni dai wasu shugabannin kasashen suka katse wasu ayyukansu domin kokarin ganin yadda za su kubutar da Mutanen kasarsu.

Mayakan dai sun bukaci dakarun Algeria su fice daga yankin kafin su bayar da damar tattaunawa, kamar yadda Abu al Baraa ya shaidawa kafar yada labaran Telebijin ta Aljazeera.

Batun garkuwa da Ma’aikatan mai ya sa kasashen yammaci kaddamar da yaki domin kakkabe mayaka a Arewacin Afrika.

Tun a watan Afrilun bara ne Mayakan Ansar dine suka karbe ikon yankin Arewacin Mali wanda hakan yasa Faransa ta kaddamar da yaki domin taimakawa Dakarun Mali karbe ikon yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.