Rashin lafiyar Shugaba Chavez ta tsananta, inji mataimakinsa
Mataimakin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro yace shugaba Hugo Chavez yana cikin mawuyacin halin kwance a wani asbitin sojan birnin Caracas, kwanaki goma da dawowar shugaban daga jinyar cutar Cancer, ko sankara a kasar Cuba.
Wallafawa ranar:
Nicolas Maduro, wanda ke tafiyar da gwamnatin kasar yace rashin lafiyar Hugo Chavez ta tsananta amma suna fatar ko zai rayu.
Tun bayan da ya tafi jinya a kasar Cuba a ranar 10 ga watan Disamban bara, Mutanen Venezuela suka dai na jin duriyar Chavez, wanda ya shafe fiye da shekaru 10 yana jan ragamar mulkin kasar da ke yankin latin Amurka.
Sai dai ya koma gida a cikin dare, ranar 18 ga watan Fabrairu domin ci gaba da kula lafiyar shi a gida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu