Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya bayyana yawan dukiyar da ya mallaka a duniya

A jiya Fadar shugaban kasar Amurka ta bayyana yawan dukiyar da shugaban kasar Barrack Obama ya mallaka da yawanta ya kai Euro dubu 466.297 a shekarar da ta gabata.

Shugaba Barack Obama na gabatar da jawabi
Shugaba Barack Obama na gabatar da jawabi Reed / Reuters
Talla

An dai bayyana cewa kashi 3 cikin 4 na kudaden da mazauna fadar White House suka mallaka ma’ana Obama da Matarsa sun zo masu ne daga albashinsu, a yayinda sauran ke zo wa Obama daga ‘yan kudin da ake bashi na hakkin mallakar wani littafin da ya rubuta.

A karkashin dokokin Amurka da kuma na sauran kasashen duniya, dole ne shugaban kasa da kuma wasu da ke rike da muhimman mukamai su rika bayyana wa al’ummar da suke jagoranta yawan dukiyar da suka mallaka lokaci zuwa lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.