Isa ga babban shafi
Venezuela-Amurka

Snowden zai samu mafaka a Venezuela

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya amince da bukatar ba Jami’in leken asirin Amurka Edward Snowden mafaka, wanda hakan zai taimakawa jami’in tserewa bayan ya makale sama da kwanaki 13 yana neman mafaka tashar jirgin Rasha. A kasar Nicaragua, Shugaba Daniel Ortega yace zai ba Snowden mafaka tare da tayin kula da rayuwar shi.

Masu zanga-zangar goyon bayan Edward Snowden wanda ya fallasa sirrin Amurka
Masu zanga-zangar goyon bayan Edward Snowden wanda ya fallasa sirrin Amurka AFP PHOTO/ SERGEI SUPINSKY
Talla

Snowden wanda Amurka ke nema ruwa a jallo bayan ya fallasa sirrinta, tuni aka janye katinsa na Fasfo. Kuma tun a lokacin ne ya ke gararamba.

Shafin tono bayanan Sirri na Wikileaks da aka ce yana taimakawa Snowden a sirrance, Wikileaks yace jami’in ya aika da bukatar neman mafaka a kasashe 21 da suka hada da Venezuela da Nicaragua.

Kasashen Turai da dama ne suka yi watsi da bukatar Snowden da kuma kasashen India da Brazil. Amma kasashen Latin Amurka da ke adawa da Amurka sun ce akwai bukatar a tausaya wa Jami’in. Kasashen sun hada da Argentina da Ecuador da Bolivia da Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.