Isa ga babban shafi
EU-Amurka

Kasashen Turai sun kalubalanci Amurka game da bayanan sirrin da Snowden ya fitar

Kungiyar Tarayyar Turai ta nemi kasar Amurka da ta bata amsa game da ikrarin da tsohon jami’inta Edward Snowden ya yi na cewa Amurkan ta dasa na’urorin daukar bayanai a ofisoshinta.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai,  José Manuel Barroso
Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai, José Manuel Barroso REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Kungiyar Tarayyar Turan dai ta yi amfani ne da kakkausan kalamai kuma cikin fushi wajen neman Amurkan ta bata amsa game da ikrarin Edward snowden wanda aka wallafa a wata jaridar kasar Jamus da ake kira Der Spiegel.

A cikin irin takardun sirri a cewar Jaridar wacce ta samu ta hanyar Snowden, bayanan ciki sun nuna cewa a shekarar 2010 jami’an leken asirin kasar Amurka sun saci bayanai a ofishin kungiyar Tarayyar Turai dake Washington ta hanyar makala na’urorin magana a ginin ofishin da kuma cikin na’urori masu kwakwalwa.

Takardun sirrin inji jaridar har ila yau sun nuna cewa kasar ta Amurka ta fi bin diddigin kasar Jamus fiye da duk wata kasa a kasashen Turai, inda ake tatsar bayanai daga kafofin sadarwa na email da talho da kuma sakonni da ake turawa ta wayar salula wanda yawansu ya kai rabin biliyan daya.

A wata rubutacciyar sanarwa da hukumomin kungiyar tarrayar ta turai suka fitar sun ce tuni sun tuntubi hukumomin Amurka dake birnin Washington da su yi musu bayani game da wannan rahoto.

Sai dai Mataimakin mai ba da shawara ta fuskar tsaro a Amurka, Ben Rhobe, yayin wani jawabi da ya yi a Afrika ta Kudu ya yi watsi da rahoton inda ya ce ba wani abin a zo a gani bane.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.