Isa ga babban shafi
Faransa-EU

Barroso ya mayar wa Faransa da Martani

Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya mayar wa Faransa da Martani akan zargin shi ke hura wutar rikicin siyasar kasar, Bayan wani ministan Faransa ya fito ya zargi shugabannin Tarayyar Turai da hura wutar rikicin Siyasar Faransa a dai dai lokacin da gwamnatin gurguzu ke kokarin tayar da komadar tattalin arzikin kasar.

Shugaban hukumar Turai Jose Manuel Barroso
Shugaban hukumar Turai Jose Manuel Barroso REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Shugaban hukumar Turai Manuel Barroso ya mayar da martani yana mai cewa gwamnatin Faransa ta fake ne yanzu da Tarayyar Turai sakamakon suka da ta ke fuskanta a cikin gida.

Ministan masana’antun Faransa ne ya yi zargin Barroso shi ke kara wa ‘yan bangaren masu tsanananin kishin kasa kwarin giwar ci gaba da adawa da matakan da gwamnatin gurguzu ta Hollande ke dauka.

Amma a cikin martanin, hukumar Turai tace ya dace ace shugabannin Faransa ne ya kamata su kare martabarsu maimakon yin suka.

Shugaba Hollande dai ya kare Ministansa, yana mai yin nadama da kalaman Barroso game da harakokin Faransa, Bayan ya soki Faransa na kin amincewa da matakin janye bangaren masana’antar fina fina da Talabijin a cikin yarjejeniyar kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.