Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Snowden ya aika da bukatar neman mafaka a kasashe 21

Shafin kwarmato bayanan Sirri na Wikileaks yace Edward Snowden ya aika da bukatar neman mafaka a kasashe 21 da suka hada da Cuba da Venezuela da Brazil da Indiya da China da Rasha da Jamus da Faransa da Ecuador da kuma Iceland. Akwai kuma bukatu na neman Mafaka da Wikileaks ya nema a madadin Snowden.

Edward Snowden, mutumin da Amurka ke nema ruwa a jallo
Edward Snowden, mutumin da Amurka ke nema ruwa a jallo youtube.com/screenshot RFI
Talla

Sanarwar ta Wikileaks tace an aika da bukatun ne daga kasar Rasha a wani Ofishin gwamnatin kasar da ke tashar jirgin Moscow.

Daga cikin bayanin bukatar mafakar da Wikileaks ya ke nema ga Snowden an bayyana irin hadarin da Snowden zai iya fuskanta daga Amurka.

Tuni dai, Edward Snowden da Amurka ke nema ruwa a Jallo, ya zargi shugaba Barack Obama da hana shi ‘yancinsa na samun mafakar siyasa, ganin yadda ya ke wa kasashen duniya barazana kan lamarin.

A sanarwar da ya bayar ta farko, tun lokacin da ya shiga kasar ta Rasha, Snowden yace, Obama na matsin lamba ga kasashen duniya don ganin sun ki ba shi mafaka.

Snowden ya godewa shugaban Ecuador Rafael Correa ga irin goyon bayan da ya bayar wajen ganin ya kaucewa hukumomin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.