Isa ga babban shafi
WHO

Kididdigar MDD a kan inda tsofaffi suka fi morewa da shan wahala a duniya

Wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya dake sa idanu kan rayuwa a kasashen duniya ya gabatar da sakamakon bincike na baya-bayan nan na kasashe goma da tsofaffi ke jin dadi, da kuma goma inda tsofaffi ke shan wahala.

Wani gida da ake kula da tsofaffi
Wani gida da ake kula da tsofaffi REUTERS/Thomas Peter
Talla

Binciken ya yi dubi ne akan kasashen 91 tare da kwatanta bayanan da ta tattara daga Hukumar Kiwon Lafiya ta WHO a duniya da wasu hukumomi.

Ta yi kuma la’akkari ne da kudaden shigansu, lafiyarsu da karatunsu da kuma ayyukansu tare da muhallan da suke zaune.

Kasar Sweden ce ta farko a jerin sunayen kasashen da tsofaffafi suka fi rayuwa mai kyau, kana sai kasar Norway a jeri na biyu da kuma jamus a jeri na uku.

Har ila yau Netherland ce a jeri na hudu, Canada a matsayi na biyar kana da Switzerland a jeri na shida yayin da New Zealand ke jeri na bakwai.

Kasar Amurka ce dai a jeri na takwas, Iceland a jeri na tara kana Japan na jeri na goma. Birtnaiya dai na jeri na 13 Faransa kuma na jeri na 18.

Najeriya dai na jeri na 85 yayin da Afghnistan ke jeri na 91.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.