Isa ga babban shafi
Pakistan-Amurka

Sharif ya nemi Obama ya kawo karshen amfani da jiragen yaki a Pakistan

Firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya bukaci shugaban Amurka Barack Obama ya kawo karshen amfani da jiragen yaki masu sarrafa kansu a yankunan Pakistan a lokacin da shugabannin biyu ke gana a fadar White House.

Firaministan Pakistan Nawaz Sharif yana tabewa da Shugaban Amurka Barack Obama a fadar White House
Firaministan Pakistan Nawaz Sharif yana tabewa da Shugaban Amurka Barack Obama a fadar White House REUTERS/Larry Downing
Talla

Shugabannin kasashen biyu sun yi alkawalin inganta huldarsu musamman tankiyar da ke tsakaninsu game da hare haren da Amurka ke kai wa a Pakistan da sunan farautar mayakan Taliban.

Cikin tattaunawar Obama da Sharif sun tabo batun tankiyar da ke tsakanin Pakistan da India akan yankin Kashmir da suke takaddama.

Wannan kuma na zuwa ne sa’o’I kalilan da kasar India ta yi zargin dakarun Pakistan sun bude wa mutanenta wuta a Kashmir.

Rahotanni sun ce an samu mutuwar Sojan India guda tare da raunata wasu guda shida.

Huldar Amurka da Pakistan dai ta kara gurguncewa ne shekaru biyu da suka gabata bayan da dakarun Amurka suka kai wani samame inda suka kashe Osama Bin Laden a Abbottabad ba tare da sanin gwamnatin Pakistan ba.

Kuma akwai hare haren jiragen sama da Amurka ke kai wa a yankunan Pakistan wanda ke rutsawa da dakarun kasar musamman a kan iyakokin kasar da Afghanistan.

A Ziyarar Sharif a Washington, Shugaba Obama ya yi alkwalin inganta huldar su da Pakistan tare da kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.