Isa ga babban shafi
Amurka-Pakistan

Obama zai gana da Sharif na Pakistan

A karon Farko, Shugaban Amurka Barack Obama zai gana da Firaministan kasar Pakistan Nawaz Sharif, inda ake sa ran batun hare haren da Amurka ke kai wa da jiragen yaki masu sarrafa kansu shi ne zai mamaye zaman tattaunawar shugabannin biyu da kuma batun kawancensu da Afghanistan.

A Washington, Nawaz Sharif yana ganawa da  John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka
A Washington, Nawaz Sharif yana ganawa da John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Wannan ne karon farko da shugaban Amurka zai gana da shugaban Pakistan tun a shekarar 2009.

Amurka tana kokarin farfado da kawancenta ne da Pakistan saboda sabani da suka samu a wani samamen dakarun Amurka da suka kashe Osama bin Laden.

Akwai tallafin kudade sama da dala Miliyan $300 da gwamnatin Obama za ta ba Paskitan.

Amma Duk da wannan har yanzu akwai barazana da rashin jutuwa tsakanin kasashen biyu musamman game da hare haren Amurka da jiragen yaki masu sarrafa kansu. Sharif ya nemi a kawo karshen amfani da jiragen kamar yadda wani rahoton kungiyar Amnesty ya kalubalanci amfani da jiragen da sunan sabawa dokokin duniya saboda suna kashe bayin Allah.

Kafin ganawar shugabannin biyu Sharif ya yi fatar kulla sabon kawance mai dorewa da Amurka.

Wani batu kuma shi ne rikicin Afghanistan da ke makwabtaka da Pakistan, wadanda dukkaninsu ke mu’amula da Amurka saboda yaki da Taliban.

Shugaba Sharif ya bayyana fatar samun zaman lafiya a Afghanistan duk da zargin da ake wa Pakistan tana taimakawa Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.