Mutuwar Jarirai na karuwa a duniya
Kungiyar agaji ta Save The Children tace Miliyoyan Jarirai ne ke mutuwa a lokacin da aka haifesu a duk shekara tare da kira ga gwamnatoci su dauki matakai. Rahoton kungiyar yace kimanin yara Miliyan 6.6 ne suka mutu a duniya a shekara ta 2012 kafin su cika shekaru biyar. Kungiyar ta danganta matsalar da rashin kulawa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar Save The Children tace ana iya kare rayukan yaran idan aka magance matsalolin da ke haifar da yawan mace-macen.
Kasar Pakistan ce aka bayyana a sahun gaba da matsalar yawan mace-macen kananan yara ta yi kamari, sai Najeriya a matsayi na biyu. Sai kuma Saliyo da Somila da Guinea-Bissau da Afghanistan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu