Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya ta saka ‘Yan Uwa musulmi na Masar cikin ‘Yan ta’adda

Gwamnatin kasar Saudiya ta saka Jam’iyyar 'Yan Uwa musulmi ta Mohammed Morsi a Masar a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda tare da Kungiyar al Nusra ta Syria, kamar yadda kafar yada labaran Al-Arabiya ta ruwaito.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama yana gaisawa da Sarki Abdallah na Saudiya
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama yana gaisawa da Sarki Abdallah na Saudiya
Talla

Saudiya ta kuma bukaci ‘Yan kasarta da ke yaki a kasashen waje su dawo gida nan da kwanaki 15 ko su fuskanci hukuncin dauri a gidan yari.

Wannan matakin  wani yunkuri ne na ci gaba da karya ayyukan Kungiyar ‘Yan uwa Musulmi a Masar.

Baya ga Brotherhood da Nusra, Saudiya kuma ta saka Kungiyar da ke fafutikar kafa kasar Musulunci a kasar Iraqi cikin jerin ‘Yan ta’adda da kungiyar Huthi da ke yaki a arewacin kasar Yemen, Mayakan da ake wa lakabi da sunan Hezbollah a yankin Hijaz.

Kasashen sunni da ke mulkin gargajiya irinsu Saudiya da Bahraine da Kuwait a kasashen Larabawa sun dade suna kyamatar ayyukan ‘Yan uwa Musulmi a Masar, domin tsoron manufofinsu na iya kawo karshen mulkinsu.

Saudiya tana cikin manyan kasashen Larabawa da ke goyon bayan ‘Yan tawayen Syria wadanda ke yaki da shugaba Bashar al Assad, kuma akwai mayaka da dama daga Saudiya da suka je yaki a Syria.

A watan jiya ne Sarki Abdallah ya amince da dokar hukuncin daurin shekaru 20 ga duk dan kasa da aka samu yana da alaka da kungiyar ‘Yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.