Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka-Turai

Crimea: Rasha ta yi gargadi ga kasashen Yamma

Sakataren harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya shaidawa takwaransa na Amurka John Kerry ta wayar tarho cewa Rasha ba zata aminta da takunkumin kasashen yammaci ba game da ‘yancin Crimea tare da yin barazanar daukar mataki mai tsauri.

Wata mata dauke da janjiri a kusa da dakarun Soji a yankin Crimea da ake takaddama
Wata mata dauke da janjiri a kusa da dakarun Soji a yankin Crimea da ake takaddama REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

“Ba zamu aminta da takunkumin Amurka da kasashen yammacin Turai ba” Mr Lavrov ya shaidawa Kerry a lokacin da suka tattaunawa ta wayar tarho.

Wannan gargadin na zuwa ne bayan gwamnatin Rasha ta amince da ‘Yancin Crimea da mutanen yankin suka kada kuri’ar ballewa daga Ukraine da ke fama da rikicin siyasa.

A ranar Litinin ne Amurka da kasashen yamma suka kakabawa wasu manyan jami’an Rasha da Ukraine takunkumi wadanda suka yi ruwa da tsaki ga ballewar yankin Crimea zuwa Rasha.

Kuma har yanzu kasashen yamma na ci gaba da caccakar Rasha akan amincewa da yankin Crimea a matsayin yanki mai cin gashin kai a Tarayyar Rasha.

Amma cikin tattaunawarsu ta wayar Tarho, Mr Lavrov ya shaidawa Kerry cewa mutanen Crimea sun zabi makomarsu ne bisa tsarin dimokuradiya karkashin dokokin duniya.

Ana dai fargabar rikicin Crimea na iya zafafa tsakanin kasashe yamma da Rasha akan makomar Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.